Ƙungiyar matasan ƙabilar Ijaw ta buƙaci Tinubu ya sauke Wike

Ƙungiyar matasan al’ummar ƙabilar Ijaw ta yi kira da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauke Nyesom Wike daga ministan Abuja.

Shugaban ƙungiyar, Alaye Theophilus ne ya bayyana kiran yayin wani jawabi da yake yi wa manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.

Mista Theophilus ya kuma yi allah wadai game da yunƙurin ƴan majalisar dokokin jihar na tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Shugaban ƙungiyar ya ce matakin ya saɓa wa muradun al’ummar jihar mai dimbin razikin man fetur.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar ta sake ƙaddamar da yunkurin tsige gwamnan.

Ba wannan ne karo na farko da ake kiran da  sauke Wike daga muƙaminsa ba.

Ko a yan kwanakin nan ma sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, ya yi kira ga ministan da ya ajiye muƙaminsa, sakamakon zarginsa da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar APC a jihar Rivers

You might also like
Leave a comment