Ƴan kasuwa na zanga-zangar karyewar darajar kuɗin Iran
An shiga kwana na biyu da ƴan kasuwa da masu tsaron shaguna suka fito tituna domin yin zanga-zanga a birnin Tehran, inda suke zanga-zanga kan yadda darajar kuɗin ƙasar ke durƙushewa.
Hotuna da bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, sun nuna ƴan kasuwar sun yi dirshan a yankin kasuwancin Iran suna rera waƙoƙin ƙin jinin gwamnatin shugaba Mas’oud Pezeshkian.
Hukumomi sun yi kakkausan gargadi kan zanga-zangar, da sauya gwamnan babban bankin ƙasar amma duk da haka ƴan ƙasar sun yi biris.
Darajar Riyal ɗin ƙasar Iran ta faɗi da kusan kashi 50 cikin 100 cikin shekara guda, lamarin da ake dangantawa da matsin lamba da takunkuman ƙasashen yamma