Ƴan majalisa sun buƙaci a jingine sabuwar dokar haraji
Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na fara aiwatar da sabuwar dokar haraji mai cike da ce-ce-ku-ce da ruɗani, har sai an kammala bincike kan zargin sauya wasu daga cikin dokokin da majalisar ta amince da su.
Ɓangaren marasa rinjaye a majalisar sun bayyana bukatar dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji domin gudanar da bincike mai inganci, wanda majalisar ta kafa don gano gaskiyar batun.
Wannan kiran ya biyo bayan zargin cewa an sauya wasu sassa na dokokin haraji bayan da majalisar ta amince da su, wanda hakan ya janyo mummunan ruɗani a tsakanin sassan gwamnati da ƴan Najeriya.
Zarge-zargen sun samo asali ne daga bambance-bambancen da aka samu tsakanin dokokin da majalisar ta amince da su da kuma waɗanda shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu a kai.
A halin yanzu, ɗaya daga cikin shugabannin majalisar, ya bayyana cewa akwai bukatar a tabbatar da gaskiyar wannan al’amari kafin a ci gaba da aiwatar da dokar.
Duk da haka, ɓangaren gwamnatin ya nesanta kansa daga zargin, inda ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sabuwar dokar haraji za ta fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, kuma akwai haɗin kai tsakanin gwamnati da majalisar kan wannan lamari.
Ministan ya kuma ce, idan akwai wata matsala, to daga ɓangaren majalisar ne.
A yanzu haka, majalisar ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin.