Ƴanbindiga sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

Bayanai daga jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na cewa wasu ƴanbindiga sun kai hari jihar, inda suka kashe sama da mutum 30 tare da sace wasu da dama.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya aike wa BBC ya ce ƴanbindigar waɗanda ake zargi sun fito daga dajin Kabe sun far wa Kasuwan-Daji da ke ƙauyen Demo da maraicen ranar Asabar, inda suka ƙona kasuwar tare da lalata shaguna da sace kayan abinci.

Sanarwar ta ci gaba da cewa da safiyar yau Lahadi ne haɗin gwiwar tawagar jami’an tsaro suka ziyarci yankin, kasancewar sun samu rahoton harin cikin dare.

”A lokacin ziyarar jami’an tsaron sun tarar da sama da mutum 30 da ƴanbindigar suka kashe, yayin da suka samu labarin sace wasu”, a cewar sanarwar.

Jami’an tsaron sun tabbatar da cewa suna bakin ƙoƙarinsu don ganin sun kuɓutar da mutanen da ƴanbindigar suka sace.

Jihar Neja na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴanbindiga.

Ko a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ma wasu mahara sun far wa makarantar sakandiren Papiri tare da sace ɗalibai fiye da 300, kodayake daga baya sun sako su.

 

You might also like
Leave a comment