Ƴansanda a Katsina sun kama mutum uku kan zargin mallakar ababen fashewa
Rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta ce ta cafke wasu mutum uku waɗanda ake zargi da mallakar tarin abubuwan fashewa.
An kama abubuwan fashewar ne a cikin wata mota ƙirar Golf a ƙauyen Koza da ke karamar hukumar Daura na jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya fitar, ya ce an samu nasarar ce bayan wani samame ranar 7 ga watan Janairun 2026, bayan cafke motar wanda wani mai suna Jamilu ke tuka wa.
Sadiq ya ce bayan binciken da suka yi, sun gano ababen fashewa 6,975 a wajen mutanen da ake zargi.
Ya ce mutanen sun amsa cewa sun karɓi ababen ne wajen wani mutum Najib, wanda aka yi niyyar kai wa Kwangolam a karamar hukumar Mai’adua na jihar Katsina daga Kano.
“Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma nan ba da jimawa ba za a tura su zuwa kotu da zarar an kammala bincike, yayin da ake ƙoƙarin ganin an kama waɗanda suke tsere,” in ji kakakin ƴansandan.