Ƴansanda sun daƙile harin ƴanbindiga a Zamfara

Rundunar ƴansanda a jihar Zamfara ta ce ta daƙile wani yunkurin ƴanbindiga na kai hari a karamar hukumar Maru na jihar a safiyar yau Lahadi.

Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce sun samu nasarar daƙile yunkurin ne bayan samun bayanan sirri.

Haɗakar jami’an tsaro ne da ya haɗa ƴansanda, sojoji, rundunar tsaro ta al’umma da kuma ƴan sa-kai suka fafata da maharan, abin da ya tilasta musu tserewa tare da raunuka. Babu wanda ya mutu ko kuma garkuwa da aka yi, acewar  sanarwar ƴansandan.

Sai dai, an tsaurara matakan tsaro a karamar hukumar ta Maru da kuma yankuna da ke ƙewaye.

Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba ya tabbatarwa al’umma cewa a shirye jami’an tsaro suke wajen kare rayuka da kuma dukiyoyinsu, inda ya buƙace su da su ci gaba da bai wa hukumomi haɗin kai

You might also like
Leave a comment