Gwamnatin Jihar Gombe ta raba jimillar naira miliyan 14 ga iyalan ‘yan jarida bakwai da suka rasu a wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Billiri–Kumo.
Hatsarin ya faru ne a ranar Litinin, 29 ga Disamba, 2025, yayin da ‘yan jaridar ke dawowa daga bikin aure na wani abokin aikinsu a Ƙaramar Hukumar Kaltungo.
Kowane iyali ya karɓi naira miliyan biyu a matsayin tallafin rage radadin jana’iza da sauran buƙatu, matakin da ya zo a ƙarƙashin ƙudurin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na tallafa wa iyalan da abin ya shafa.
Da yake wakiltar gwamnan a wajen rabon tallafin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa gwamnatin ta riga ta bayar da tallafin farko ga waɗanda suka jikkata, tare da ɗaukar nauyin dukkan kuɗaɗen jinya da kulawar asibiti.
Farfesa Njodi ya bayyana alhininsa kan asarar da aka yi, yana mai jaddada cewa tallafin ba diyya ba ne, illa wata alama ta tausayi da goyon baya a wannan lokaci mai wahala.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya Abdullahi, ya yabawa gwamnatin Gombe kan matakin da ya kira na gaggawa da jinƙai, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da inshorar rai da lafiya ga ‘yan jarida.
Haka kuma,
Daraktan NTA Gombe, Abubakar Adamu, ya miƙa godiyarsa ga Darakta Janar na NTA da gwamnan kan wannan mataki.
Da yake magana a madadin iyalan da suka rasu, Lauya Abubakar Ahmed ya bayyana tallafin a matsayin na farko irinsa a tarihin jihar, yana mai addu’ar Allah Ya saka wa gwamna da gwamnatinsa da alheri