Ɗan Kwankwaso da wasu kwamishinonin Kano sun fara kauracewa ofisoshinsu gabanin sauya sheƙar gwamna Abba
Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewa Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Kwankwaso, ya fara kwashe kayansa daga ofishinsa, wanda hakan ke nuni da tsanantar rikicin siyasa a cikin jam’iyyar NNPP a jihar.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheka daga jam’iyyar.
Mustapha Kwankwaso, wanda kuma babban ɗan tsohon gwamnan Kano ne kuma jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, bai gabatar da takardar ajiye aiki a hukumance ba.
Haka kuma, gwamnan bai sanar da cire shi daga muƙaminsa ba. Sai dai majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa ana sa ran Mustapha zai yi murabus kafin ko bayan Gwamna Yusuf ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar.
Haryanzu dai Gwamna Abba Yusuf bai fito fili ya tabbatar da sauya sheƙarsa ba, wasu daga cikin makusantansa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar sun tabbatar da shirin ficewarsu daga NNPP.
Ana Dai danganta wannan mataki da rikice-rikicen shari’a da ke ci gaba da kamari a cikin jam’iyyar, wanda hakan ke barazana ga makomar siyasar su.
Wata majiya daga gwamnatin Kano sun shaida wa jaridar PREMIUM TIMES cewa Mustapha Kwankwaso ya bar ma’aikatarsa tare da kwashe kayansa bayan da mahaifinsa, Rabiu Kwankwaso, ya nuna rashin amincewa da shirin gwamnan na sauya sheƙa.
Wannan ya nuna rarrabuwar kawuna a cikin tafiyar Kwankwasiyya, wadda ta kasance ginshikin siyasar jihar Kano.
Mustapha kwankwaso da wasu kwamishinonin Kano sun fara kauracewa ofisoshinsu gabanin sauya sheƙar gwamna Abba