Gwamnatin Jihar kano ta shiryawa Yan jaridar yanar gizo Taron karawa juna sani na kwana biyu a Jahar jigawa
Gwamnatin Jihar Kano ta shirya Bitar kwana biyu ga Yan jaridar yanar gizo a jahar jigawa don jaddada inganci aikin jaridar yanar gizo bisa gaskiya da da,a afadin jahar, inda ta bayyana kafafen yaɗa labaran a matsayin ginshiƙi wajen tafiyar da dimokuraɗiyya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya, shine ya bayyana hakan a ranar Laraba 14-1-2026 yayin da yake bayani awajen taron horaswa a Dakin taro na man power development institute dutse na kwanaki biyu ga mambobin kafafen yada labarai na zamani [Kano Online Media Chapel]
Waiya yace an shirya horon ne saboda goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano, don basu horo na musamman akan harkar jaridar yanar gizo.
Waiya ya Kara da cewa wannan horo, shi ne irinsa na farko ga masu wallafa jaridun intanet a Jihar Kano, inda ya nuna yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke kallon aikin jarida a matsayin Wani ɓangare na tafiyar da ayyukan dimokuraɗiyya.
Akarshe Kwamishinan ya yi kira ga ‘yan jaridar masu wallafa labarai ta yanar gizo da su riƙa bin ƙa’idojin aikin da nuna ƙwarewa da gaskiya wajen tattarawa da yaɗa labarai.
Anasa bangaren Mukaddashi Babban Sakatare na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Usman Bello, ya ce gwamnati ta amince da gudanar da taron ne a wajen jihar Kano sakamakon muhimmancin da aikin jaridar yabar gizo ke Dashi.