DA ƊUMI-ƊUMI: BomTa Fashe a Cikin Masallaci a Kasuwar Maiduguri, Masu Ibada Sun Mutu
Fashewar Boma a Masallaci a Maiduguri
A ranar Laraba, an samu fashewar boma a cikin wani masallaci da ke Kasuwa Gamboru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wani masani kan tsaro da yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi da Yammacin Afirka, Zagazola Makama, ya bayyana cewa fashewar ta auku ne yayin da mutane ke salla, inda hakan ya janyo firgici da rudani a cikin kasuwar.
Wasu shaidu sun ce bomar ta tarwatsa wani ɓangare na masallacin, inda ta kashe wasu nan take, sannan ta raunata wasu da dama.
