Akalla yan jariada 44 akasace wasu aka tsare a habasha a shekara 2025; Rahoton IMS

Rahoton ya bayyana cewa an samu ƙaruwar kai wa ƴan jarida hare-hare, da kamun ba gaira ba dalili, da kuma barazanar kuɗi ga ’yan jarida da gidajen watsa labarai.

 

 

 

 

 

Binciken ya nuna cewa matsin lamba kan kafafen yaɗa labarai ya ci gaba kamar yadda aka gani a 2024, lokacin da aka daure ’yan jarida 43.

 

 

 

 

Kungiyar ta bayyana shekarar 2025 a matsayin lokaci mai matuƙar damuwa ga ’yan jaridar ƙasar, sakamakon yawaitar tsare-tsare da sace-sace da muzgunawa da suke fuskanta.

 

 

 

 

 

 

Rahoton ya kuma bayyana irin haɗurran da sassa daban-daban na kafafen watsa labarai ke fuskanta yayin da suke aiki a yanayi mai ƙara zama haɗari, wanda matsalolin siyasa da dokoki da tsaro, da tattalin arziki ke haddasawa.

 

 

 

 

 

You might also like
Leave a comment