Akpabio Ya Janye Karar  Da Ya Shigar Kan Natasha

 

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya janye ƙarar batanci da ya shigar a gaban kotu kan Natasha, tare da dukkan sauran ƙararrakin da ya gabatar a baya, bayan sauraron wa’azi na ƙarshen shekara da ya shafi muhimmancin yafiya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a farkon sabuwar shekarar 2026, Akpabio ya bayyana cewa shawarar janye ƙarar ta biyo bayan nasiha da limamin cocinsa ya yi, inda ya ja hankalin mabiya kan buƙatar yafiya, sulhu da sabuwar fahimta yayin shiga sabuwar shekara

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce ya ɗauki matakin ne domin nuna koyi da koyarwar addini, tare da mayar da hankali kan haɗin kai, zaman lafiya da cigaban ƙasa, maimakon ci gaba da rikice-rikicen shari’a.

Akpabio ya umarci lauyoyinsa da su gaggauta janye dukkanin ƙararraki guda tara da ya shigar a gaban kotu, yana mai jaddada cewa ya yi hakan ne a matsayin kyautar sabuwar shekara, tare da fatan sabon shafi na fahimta da mutunta juna zai buɗe tsakaninsa da waɗanda abin ya shafa.

You might also like
Leave a comment