Amurka na shirin ƙwace Greenland
Fadar gwamnatin Amurka ta ce Shugaba Donald Trump tare da manyan jami’an gwamnatinsa na tattauna hanyoyi daban-daban da Amurka za ta iya mallakar yankin Greenland.
Fadar ta bayyana cewa amfani da ƙarfin soji na daga cikin zaɓuɓɓukan da ake duba.
Mai magana da yawun Shugaba Trump, Karoline Leavitt, ta ce shugaban ya fito ƙarara cewa wannan mataki na da nasaba da tsaron ƙasa, yana mai cewa zai taimaka wajen kange makiyan Amurka a yankin.
A nasa ɓangaren, Firaministan yankin ya yi maraba da sanarwar haɗin gwiwa da shugabannin Turai suka fitar, wadda ta jaddada aniyar kare dokokin duniya da ‘yancin cin gashin kai na Greenland, wanda ke ƙarƙashin ƙasar Denmark.