Amurka ta Koma Sa Ido a Dajin Sambisa Bayan Hare-haren Sama a Sakkwato
Kasar Amurka ta sake komawa gudanar da ayyukan tattara bayanan sirri da sa ido a Najeriya a ranar Asabar, biyo bayan hare-haren da aka kai wa ‘yan ta’addar ISIS a Sakkwato a daren ranar Alhamis.
Brant Philip, wani mai bin diddigin ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, ya raba bayanan bin diddigin jiragen sama da suka nuna jirgin yana shawagi a jihar Borno.
Bayanai hakan sun nuna cewa jirgin kirar Gulfstream V ne, wani jirgin kasuwanci mai dogon zango wanda galibi ake yi masa gyaran fuska domin ayyukan tattara bayanan sirri, da kuma bincike.
Philip ya ce ayyukan tattara bayanan sirri na ranar Asabar sun mayar da hankali ne kan kungiyar ISWAP reshen ISIS a Najeriya, wacce ke gudanar da ayyukanta galibi a yankin arewa maso gabas da kuma tafkin Chadi.