Amurka ta tsare shugaba Maduro a gidan yarin New York

Kafofin ya ɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa ana tsare da shugaban Venezueal, Nicolas Maduro da Amurka ta kama a gidan yarin New York.

Gidan yarin ya yi fice wajen ajiye manyan fursunoni ciki har da Ghislaine Maxwell Ba’amurka ɗan asalin Birtaniya da aka samu da laifin safarar ƙananan ƴan mata domin karuwanci a 2021 da kuma Sean ‘Diddy’ Combs, fitaccen mawaƙin gambara na Amurka.

Kawo yanzu dai ba a san inda matarsa tasa take ba.

A ranar Asabar ne dai Amurka da kama shugaba Maduro da matarsa bayn ƙaddamar da manyan hare-hare a ƙasar.

Inda daga baya aka gurfanar da shi a Amurka kan tuhumar zargin safarar miyagun ƙwayoyi da makamai.

Tuni shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da jagorantar Venezuela har zuwa lokacin kafa gwamnati

 

You might also like
Leave a comment