An buɗe Sakandiren Ƴanmata ta Maga watanni biyu bayan kai wa makaratarhari
Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da sake buɗe makarantar Sakandiren ƴanmata ta Maga, inda aka sace ƴanmata 24 kafin daga baya a ceto su.
Kwamishiniyar makarantun Firamare da Sakandare a jihar, Dakta Halima Bande, ita ce ta bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro kan tsaro da shugabannin makarantu a birnin Kebbi.
Bande ta bayyana cewa al’amura sun fara komawa daidai kuma an karfafawa iyaye da ɗalibai gwiwa ta hanyar shawarwari da kuma aika jami’an tsaro – lamarin da ya buɗe kofar komawa don cigaba da karatu.
Kwamishiniyar ta ce gwamnati na shirye wajen ɗaukar matakan tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar ɗalibai da malamai.
A cewarta, gwamna Nasir Idris ya bayar da umarnin aiwatar da shirye-shiryen wayar da kan shugabannin makarantu da kuma malamai kan tsaro domin kauce wa afkuwar abin da ya faru a nan gaba.
“Shugabannin makarantu, mataimakansu, malamai da kuma ɗalibai na da rawar taka wa wajen tabbatar da tsaro a makarantu,” in ji dakta Halima.