An Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Rajin Ganin Kasar Yarabawa Ta Ware A Jihar Ogun

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun  ta sanar da kama mutane takwas da ake zargi da rajin ganin yankinsu ya balle daga Najeriya, bisa zargin tada zaune tsaye,  tare da tare hanyoyin ababen hawa da kuma kai wa jami’an ’yan sanda hari. Anbayar da rahoton cewa an kama wadanda ake zargin ne a jiya alhamis a mahadar Temidire da kuma karkashin gadar Sango-Ota da ke Jihar Ogun, yayin da suke gudanar da zanga-zanga a karkashin kungiyar da suka kira “Democratic Republic of the Yoruba.”A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Oluseyi Babaseyi ya fitar, ya bayyana cewa mambobin kungiyar sun tare hanyoyi ba bisa ka’ida ba, inda suka kunna wuta a kan titi, suka hana zirga-zirgar ababen hawa, sannan suka kai wa jami’an ’yan sanda hari wadanda aka tura don tabbatar da doka da oda.Babaseyi ya bayyana a cikin sanarwar da aka raba wa manema labarai.sun Sami rohoton Inda  jami’an ’yan sanda sun gaggauta isa wuraren da abin ya shafa, inda suka yi nasarar tarwatsa kungiyar.”Ya Kuma kara da cewa bayan tarwatsa su, jami’an rundunar sun Kuma   wadanda ake zargin kamar haka:•Adewale Sosanya, namiji mai shekaru 48•Opeyemi Oladotun, namiji mai shekaru 31•Zara Gabriel, mace mai shekaru 22•Ajoke Gabriel, mace mai shekaru 19•Adewale Adebomojo, mace mai shekaru 48•Yusuf Tanimowo, namiji mai shekaru 40•Olurotimi Ademola, namiji mai shekaru 52•Toyin Gabriel, mace mai shekaru 40A Sai Kuma  kayayyakin da aka kwato sun hada da mota kirar Toyota Dyna da aka yi amfani da ita wajen jigilar wadanda ake zargin, lasifika guda biyu, katon da ke dauke da tutoci, riguna masu dauke da rubuce-rubucen rajin da suke yi, da kuma tutoci masu dauke da sakonninsu da manufofinsu.Ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Babaseyi ya rawaito cewa Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun yana sake tabbatar wa mazauna jihar kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyinsu Haka kuma,

Kwamishinan ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta amince da duk wani mataki da zai iya dagula zaman lafiyar jama’a ba, yana mai jaddada cewa duk wani hari da aka kai wa jami’an ’yan sanda za a dauki kwararan matakai a kansa. Ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda tare da kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba ta lambobin gaggawa na rundunar ’yan sandan Jihar Ogun.

You might also like
Leave a comment