An miƙa wa hukumomin jihar Neja ɗalibai 130 da aka ceto
An miƙa ɗaliban nan su ɗari da talatin da aka ceto daga hannun masu garkuwa da su zuwa hannun hukumomi a jihar Neja.
Gwamnan jihar, da wasu manyan jam’ian gwamnati ne suka tarbe su a fadar gwamnati da ke babban birnin jihar Minna bayan da suka iso a motoci shida tare da rakiyar jami’an tsaro.
Hukumomi a Kasar sun ce an ceto yaran ne yayin wani aiki na musamman da jami’an tsaro suka yi, duk da ba su bayar da karin bayani ba.
Hukumomi sun ce ɗaliban, da malamai bakwai da aka ceto, su kadai ne suka rage a hannun ƴan bindigar cikin waɗanda aka sace daga makarantar kwana ta Katolika ta St Mary da ke Papiri a watan Nuwamba.