Anfara sauraron ƙarar neman belin tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami
Kotun tarayya da ke Samantha a babbar birnin tarayya Abuja ta fara sauraron ƙara kan neman belin tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda ke tsare a gidan yari na Kuje da ke Abuja.
Malami tare da ɗansa Abdulaziz da ɗaya daga cikin matansa, Bashir Asabe, suna fuskantar shari’a ne kan zargin halasta kuɗaɗen haramun bisa tuhume-tuhume 16 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta shigar a kansu.
Ana dai zargin su da halasta kuɗaɗen haram har naira biliyan 8.7 inda dukkaninsu suka musanta zargin lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu a ranar 29 ga Disamba, 2025.
Bayan musanta laifin, mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin tsare su a gidan yarin Kuje har zuwa ranar 2 ga Janairu, 2026, inda kotun za ta saurari ƙarar neman belinsu a rubuce da lauyoyinsu suka shigar.