Anrantsar da musulmi na farko Magajin garin new york-mamdani zohran
A ranar 1 ga watan Janairun nan na sabuwar shekarar 2026 aka rantsar da Zohran Mamdani a matsayin Magajin garin New York, inda ya kafa tarihin zama Musulmi na farko da ya riƙe ofishin sannan kuma mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe kujerar a fiye da ƙarni.
Ya kasance Magajin garin na New York na 111 kuma alƙalin alƙalan birnin, Letitia James ce ta jagorancin bikin rantsarwar a farkon daren ranar 1 ga sabuwar shekarar 2026.
A watan Nuwamba ne dai matashin mai shekaru 34 ya kafa tarihi inda ya lashe zaɓen zama Magajin garin na birnin New York.
Zaɓen bana ya jawo hankalin jama’a sosai. Mamdani, mai shekaru 34, wanda dan majalisar dokoki ne a jihar New York inda ya fara shekarar ba tare da sanin jama’a sosai ba, amma daga baya ya zama sananne.
Wannan nasara tana nuna sabon salo ga masu ra’ayin cigaba, kuma tana nuna sauyin tunanin siyasa a birnin.
Wane ne Zohran Mamdani, Musulmi na farko Magajin garin birnin New York?
An rantsar da Zohran Mamdani a matsayin Magajin garin birnin New York