Babban hafsan sojin ƙasa ya ziyarci Babangida da Abdulsalam
Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya kai ziyarar girmamawa ga tsofaffin shugabannin ƙasa, Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, tare da ziyartar Gwamnatin Jihar Neja, domin ƙarfafa haɗin gwiwar farar hula da sojoji da inganta tsaro.
Ziyarorin, da suka gudana a Minna, sun nuna ƙudirin rundunar sojin ƙasa na inganta horo, shirye-shiryen aiki da haɗin kai da shugabannin siyasa da gwamnatocin jihohi wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.
Shaibu ya bayyana muhimmancin Jihar Nijar a tsarin tsaron ƙasa, yana mai cewa rundunar na amfani da dukkan albarkatu da fasaha domin magance matsalolin tsaro.
Ya kuma kai ziyarar aiki ga Rundunonin 31 da 11 da 18 a Bida domin tantance kalubalen aiki da ƙarfafa rundunonin da ke bakin aiki.
A martaninsu, Babangida da Abdulsalami sun yaba da jagorancin Shaibu, tare da yi masa addu’ar samun nasara yayin da yake jagorantar Rundunar Sojin ƙasa ta Najeriya.