Babban Layin Wutar Lantarki na Kasa Ya Sake Durkushewa
Babban layin wutar lantarki na Najeriya ya sake durkushewa, lamarin da ya jefa birane da dama cikin duhu.Bincike a shafin yanar gizon Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Najeriya (NISO) ta sanaar da cewa wutar da ake samarwa a kowace sa’a ta ragu sosai daga megawatt 2660.77 da misalin karfe 2 na rana zuwa megawatt 139.92 zuwa karfe 3 na rana.Tashar samar da wutar lantarki ta ruwa ta Shiroro da tashar gas dake Delta ce kadai ke ba da gudummawa ga layin wutar a lokacin.Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa ta maido da cikakken samar da wutar lantarki ga layin wutar biyo bayan lalata bututun gas na Lagos-Escravos, wanda shi ne babban hanyar samar da gas ga tashoshin wutar lantarki da dama a kasarnan.