Baza,a Cire Kudi Kai-tsaye Daga Asusun Banki a Karkashin Sabbin Dokokin Haraji – Oyedele
Shugaban Kwamitin, Shugaban Kasa kan Manufofin Kasafi da Gyaran Haraji, Mista Taiwo Oyedele ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sabbin dokokin haraji da za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, ba za su hada da cire kudi kai-tsaye daga asusun banki na mutane ba. Ya bayyana cewa wadannan sauye-sauye sun dogara ne kan bayyana kudin shiga da mutum ya yi da kansa, maimakon cire kudi ta karfin tsiya daga banki.
Mista Oyedele ya bayar da wannan tabbacin ne yayin wani shirin gidan talabijin na Channels mai suna 2025 In Retrospect: Charting a Pathway 2026 wanda aka yada a ranar Talata.
A yayin shirin, Oyedele ya karyata ikirarin da ake yi na cewa gwamnati za ta rika sanya ido ko cire kudi daga asusun banki na daidaikun mutane. Ya jaddada cewa abin da ake bukata kawai shi ne masu biyan haraji su bayyana yawan kudin shigar da suka samu a karshen shekarar haraji.
“Mutane suna tunanin cewa gwamnati za ta rika cire kudi daga asusun bankinsu daga shekara mai zuwa, kuma ban san ma yadda aka yi suka zo da wannan tunanin ba. Babu wanda zai cire kudi daga asusunka a kan duk wani kudi da ka tura. Ko biliyan daya ne ko kuma naira dubu daya, a karshen shekara, kai da kanka za ka gaya wa gwamnati abin da ka samu,” in ji shi.
Wannan bayani na zuwa ne domin kwantar da hankulan jama’a game da rade-raden da ake yi kan yadda sabon tsarin harajin zai shafi talakawa da masu kananan sana’o’i a fadin kasar.