Da dumi dumi DSS Ta Saki Walida
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karɓi Walida Abdulhadi Ibrahim wacce ta ɓace tun shekarar 2023 kuma take a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).
Gwamnan ya tabbatar da cewa za a tabbatar da adalci kan zargin sace ta da aka yi.
Gwamna Namadi, tare da wasu jami’an gwamnati, ya karɓi Walida daga DSS a birnin Abuja. Duk da cewa iyayenta ba su halarci wajen karɓar ta ba, wakilan ƙungiyoyin fararen hula da kuma ‘yan jarida sun kasance a wurin.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wata mai suna Mariam da sace Walida tare da gallaza mata, kafin daga bisani wani jami’in DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi ya karɓe ta, inda aka ce ta haifi diya mace a watan Nuwamba 2025. Bayan yunƙurin da danginta suka yi na kwato ta bai yi nasara ba, sai aka bi ta hanyar shari’a wanda ya kai ga sakinta daga hannun DSS.
Gwamna Namadi ya jaddada cewa tsaron Walida shi ne a gaba, yana mai cewa za ta ci gaba da kasancewa karkashin kulawar gwamnatin jihar a Abuja har sai an kammala dukkan lamurran shari’a.
Babban Daraktan DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, ya tabbatar da cewa Ifeanyi an ci gaba da tsareshi domin gudanar da bincike.
A nasa bangaren, Barrista Haroun Muhammad daga Nigerian Supreme Council of Islamic Affairs ya nuna damuwa kan yiwuwar tashe-tashen hankula na zamantakewa da ka iya tasowa sakamakon wannan lamari.