Dakarun Sojin nigeria Sun dakile wani hari. tare. da Ƙwato Dabbobi 257 A Kano

Dakarun Soji ƙarƙashin dakarun haɗin gwiwa na JTF sun ƙwato dabbobi 257 bayan daƙile wani harin ɓarayin shanu a ƙaramar hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

 

 

 

 

Aikin, wanda dakarun sojin ƙasa na Rundunar 3 Brigade ke jagoranta daga sansaninsu da ke Gwarzo, ya gudana ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 1 ga Maris, 2026.

 

 

 

Wata sanarwa da Manjo Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar ya fitar, ta ce dakarun sun amsa kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:57 na safe, inda suka yi saurin kai ɗauki zuwa wata hanyar da ake zargin ’yan bindiga ke bi.

 

 

 

 

 

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun sun yi wa wata ƙungiyar ’yan bindiga kwanton ɓauna da suka fafata da su a ƙauyen Dayi, waɗanda tun da farko aka samu rahoton sun sato dabbobi daga ƙauyen Mainika a cikin Gwarzo.

 

 

 

 

 

“’Yan bindigar waɗanda sun soma artabu da dakarun amma daga bisani suka tsere zuwa Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, inda suka bar dukkan dabbobin d
Bayanai sun ce dabbobin da aka ƙwato sun haɗa da shanu 135, tumaki 119, akuya guda ɗaya da jakuna biyu, wanda jimillarsu ta kai 257.

 

 

 

 

 

Mahukuntan sun tabbatar da cewa an miƙa dabbobin ga masu su ta hannun shugabannin al’umma da na ƙananan hukumomi, yayin da aka ce ’yan bindigar sun tafka asara mai yawa a yayin fafatawar.
Kwamandan Rundunar 3 Brigade, Birgediya Janar Ahmad Tukur, ya yaba wa dakarun bisa jarumtaka da jajircewarsu wajen gudanar da wannan aikin cikin ƙwazo da ƙwarin gwiwa.

 

 

 

 

Ya kuma gode wa al’ummar yankin bisa bayar da sahihan bayanai a kan lokaci, wanda a cewarsa ya taimaka matuƙa wajen nasarar aikin.

 

 

 

Sojojin sun tabbatar wa al’ummar yankin cewa za su ci gaba da sa ido da ƙara kaimi wajen ayyukan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

 

 

 

 

 

Aminiya ta ruwaito cewa dakarun haɗin gwiwar da ke Gwarzo na ƙunshe da jami’an sojoji, ’yan sanda, DSS, NSCDC da kuma ’yan sa-kai na al’umma.

You might also like
Leave a comment