Dakarun Sojin Sama Sunyi nasarar  Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama, da Tarwatsa maboyarsu da Cibiyar kera Bama-bamai,  A Zamfara

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) da ke aiki a karkashin Rundunar Sojan Sama ta ‘Operation FANSAN YAMMA’, Sashe na 2, a ranar 28 ga Disamba, 2025, ta kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tarwatsa sansanoninsu da cibiyar ƙera bama-bamai a Jihar Zamfara.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Sojan Sama, Air Cdre Ehimen Ejodame, ya fitar, ya ce ayyukan biyu masu karfin gaske a sansanonin Tudun Turba da na Kachalla Dogo Sule, dukkansu a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda da dama.

Air Cdre Ejodame ya ce Rundunar Sojan Saman, wacce ke aiki bisa bayanan sirri masu inganci, ta tura jiragen yakinta kan sansanonin ‘yan ta’adda a wuraren da aka tabbatar. A cewarsa, harin farko an kai ne a Tudun Turba, maɓoyar ‘yan ta’adda da aka tabbatar.

A cewar Kakakin NAF, an gudanar da harin na biyu a sansanin Kachalla Dogo Sule, wani sansani na ‘yan bindiga da aka gano a matsayin babbar cibiyar ƙerawa da kuma dasa bama-baman.

Ya ce bayanan sirrin sun danganta sansanin da dasa bama-baman da suka tashi a kwanan nan a kan hanyar Ɗan sadau zuwa Magami da ke jihar Zamfara

 

You might also like
Leave a comment