DSS ta kama jami’inta da ake zargi da sace wata yarinya a Jigawa

 

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta sanar da kama wani jami’inta da ake zargi da sace wata yarinya yar jigawa tare da tilasta mata barin addinin musulunci sannan ya rika lalata da ita har ta haihu.

A makon nan ne wata kotu a Haɗeja da ke jihar Jigawa ta bayar da umarnin kamo jami’in tare da bincikarsa kan wanna zargi da ake yi masa kan yarinyar mai shekara 16.

Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan hulda da jama’a ta hukumar ta DSS, Favour Dozie ta fitar aka kuma wallafa a shafin hukumar, DSS ta ce tana gudanar da bincike game da lamarin.

”Muna kuma tabbatar da cewa an kama jami’in mai suna Ifeanyi Onyewuenyi, ba Ifeanyi Festus ba kamar yadda umarnin kotun ya nuna”, in ji sanarwar.

Hukumar ta ce wannan ɗabi’a da ke zargin jami’in nata da aikatawa ya saɓa wa ƙa’idoji da dokokin aikin DSS, inda ta sha alwashin bayyana wa duniya sakamakon binciken da take yi kan jami’in.

Rahotonni sun ce jami’in ya sace yarinyar tsawon shekara biyu da suka gabata inda ya ci gaba da ɓoyeta a hannunsa, bayan tilasta mata komawa adinin Kirista, ya kuma riƙa lalata da ita har ta haihu.

You might also like
Leave a comment