EFCC ta Gurfanar Da Ɗan ƙasar Austria Kan Boye Wasu Maƙudan Kuɗaɗe.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da masuyiwa Tattalin Arziki Ƙasa zagon Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Austria mai suna Kavlak Onal a gaban Kotu sakamakon samun sa dauke da maƙudan kuɗaɗe wanda bai gabatar da bayyana su ba.
an chafke shi a filin jirgin saman Legas da yake ƙoƙarin hawa jirgin Emirates Airline zuwa Dubai.
Daraktan shiyya na biyu na Hukumar EFCC a Legas, ya gurfanar da Kavlak Onal a gaban Mai Shari’a Yelim Bogoro na Babbar Kotun Tarayya reshen Jahar Legas, a ranar Juma’ar data gabata.
An gano Onal ne a filin jirgin saman Legas ta hannun Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) bisa zargin gaza bayyana mallakar $800,575 da €651,505 da ke tare da shi. A yinkurinsa na hawa jirgin Emirates zuwa Dubai, sai jami’an Kwastam suka tare shi yayin bincike na yau da kullum a teburin bayyana kuɗaɗen waje (AML/CFT Currency Declaration Desk) a ranar 16 ga Disamba a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed, Legas.
Daga nan aka miƙa shi ga EFCC domin ci gaba da zurfafa bincike.
Bayan kammala bincike, an gurfanar da wanda ake tuhuma a ranar 9 ga Janairu kan tuhume-tuhume biyu na safarar kuɗaɗen haram (money laundering).
A tuhuma ta farko an tuhumeshine kamar haka, Mr. Kavlak Onal, a ranar 13 ga Disamba, a Legas, cikin ikon wannan kotu, ka gaza bayyana adadin $800,575 (Dala dubu dari takwas da dubu dari biyar da saba’in da biyar) ga Hukumar Kwastam ta Nijeriya a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed, Ikeja, Legas, don haka ka aikata laifi da ya saɓa wa doka ƙarƙashin Sashe na 3(5) na Dokar Hana fatauci da hada-hadar kuɗi ta haram da wanke Kuɗi, 2022.”
Kavlak Onal, ya ce “ba ni da laifi” ga dukkan tuhume-tuhumen da aka karanta kuma ake zargina da su”. Don haka yake roƙon Kotu ta sake shi.
lauyan gwamnati Bilikisu Bala Buhari ta roƙi kotu ta sa ranar shari’a domin gwamnati ta gabatar da hujjoji, tare da neman a tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.
Your message has been sent
Lauyan kariya, Stanley Imhanruor, ya sanar da kotu cewa ya shigar da buƙatar beli a madadin wanda yake karewa.
A martani, lauyar gwamnati ta ce an ba ta kwafin buƙatar belin da ƙarfe 9:07 na safe a ranar 9 ga Janairu, kuma tana buƙatar lokaci domin amsawa.
Saboda haka, Mai Shari’a Bogoro ya ɗage shari’ar zuwa 16 ga Janairu domin sauraron buƙatar belin, kamar yadda kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana.