EFCC tace Binciken da ake yi wa Malami ba shi da alaƙa da siyasa

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Olanipekun Olukoyede ya mayar da martani ga masu cewa hukumar na binciken tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami ne saboda ya bar jam’iyyar APC.

Olukoyede ya ce binciken da ake yi wa Malami ba shi da alaƙa da siyasa ko bambancin jam’iyya.

A cikin wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin Channels, Olukoyede ya bayyana cewa binciken Malami ya fara ne tun kafin ya karbi shugabancin hukumar.

“Tun shekarun baya da suka wuce kafin na zama shugaban hukumar aka fara binciken shi. Abin da na yi shi ne tabbatar da cewa an gudanar da binciken cikin tsari da inganci,” in ji shi.

Shugaban ya kuma nanata cewa ba za a iya ciyar da ƙasar gaba ba idan ana tsangwama saboda bambancin siyasa.

“Idan muna so Najeriya ta ci gaba, dole ne mu yarda cewa wannan yaƙin cin hanci da rashawa da hukumar ke yi cikin aikinta ne kawai kuma duk sai mun amince da yaƙar cin hanci da rashawa ba tare da ɗaukar ɓangare ba, wannan shi nake so ‘yan Najeriya su fahimta su kuma yarda da mu,” Olukoyede ya ce.

Olukoyede ya ce binciken Malami ya kasance tsawon kusan shekaru biyu da rabi, inda hukumar ke ƙoƙarin tabbatar da gaskiyar zargin da ake masa.

 

Hukumar dai ta kai Malami da iyalansa kotu kan zargin halasta kuɗaɗen haramun wanda ya kai ga kai su gidan yarin Kuje da ke Abuja amma daga bisani kotun ta bayar da belinsu kan kuɗi naira miliyan 500 tare da kawo mutum biyu a matsayin waɗanda za su tsaya musu.

You might also like
Leave a comment