EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami a Abuja a kotu
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami a gaban kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata.
Za a gurfanar da shi tare da dansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da wata mata mai suna Hajia Asabe bashir.
EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda 16 a kansu, waɗanda suka shafi safarar kuɗaɗen haramun masu girma da mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba da darajarsu ta haura Naira biliyan 8.7.
Ana zargin sun ɓoye kudaden ta hanyar asusun banki da kamfanoni da kuma sayen manyan gidaje a Abuja da wasu jihohi tsakanin shekarar 2015 zuwa 2025.
Zargin ya haɗa da amfani da kamfanoni irin su Metropolitan Auto Tech Ltd da Meethaq Hotels Ltd wajen ɓoye kudade sama da biliyan daya, da kuma sayen gidaje masu tsada a Maitama da Garki da Jabi da Asokoro da Gwarimpa.
Hukumar ta ce laifukan sun saɓawa dokar hana safarar kuɗaɗen haram na shekarun 2011 da 2022, kuma ta shirya gabatar da shaidu daga jami’an bankuna da masu canjin kudi da wakilan kamfanoni domin tabbatar da tuhume-tuhumen.