El-Rufai Zai Gurfana a Gaban EFCC a Ranar Litinin
Malam Nasir El-Rufai zai gurfana a gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da misalin karfe 10:00 na safe a ranar Litinin.
Lauyansa, Ubong Esop Akpan, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan yunkurin kama shi da aka yi a filin jirgin saman Abuja a ranar Alhamis.
Ya ce jami’an tsaro sun tunkari El-Rufai ne da yammacin ranar Alhamis bayan isowarsa Abuja ta jirgin Egypt Air mai lamba MS 877 daga birnin Alkahira na kasar Masar.
A cewarsa, wannan mataki babban take hakkin kundin tsarin mulki ne, wuce gona da iri daga bangaren zartarwa, tare da nuna rashin mutunta dokokin kasa.