Guguwa mai ƙarfi ta hallaka mutum biyu a Sweden
Wata guguwa mai ƙarfin gaske ta hallaka wasu mutum biyu a Sweden, inda ta kuma janyo tsaiko wajen tafiye-tafiye da ɗaukewar lantarki.
Hukumar lura da yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun iska mai ƙarfi a sassan arewacin ƙasar da dama yayin da guguwar mai suna Johannes ke ci gaba da ɓarna.
Wani mutum ɗan shekara 50 ya mutu bayan da itace ya faɗi a kansa a kudancin ƙasar, kamar yadda kafafen yaɗa labarai da kuma ƴansandan ƙasar suka ruwaito. Wani kamfani ma ya ce ma’aikacinsa ɗaya ya mutu a lamarin.
An samu ɗaukewar lantarki a dubun-dubatar gidaje a Sweden, Norway da kuma Finland.
A Sweden, sama da gidaje 40,000 ne lamarin na katsewar lantarki ya shafa sannan an dakatar da tafiye-tafiyen jiragen ƙasa, a cewar kamfanin dillancin labarai na Sweden TT.
Haka kuma, an soke tashin jiragen sama da jiragen ƙasa da kuma na ruwa a faɗin ƙasashen arewacin Turai.