Gwamna Zulum Ya Kaddamar da Sabbin Makarantun Sakandare Biyu, Ya Kuma Bayar da Umarnin Mayar da Makarantun Jihar na Zamani

Gwamna Zulum Ya Kaddamar da Sabbin Makarantun Sakandare Biyu, Ya Kuma Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da sabbin makarantun sakandaren gwamnati (GSSS) guda biyu da aka gina a garuruwan Fikiyel da Balbaya da ke Karamar Hukumar Bayo, a matsayin wani bangare na kokarin inganta ilimi a jihar.Haka zalika, gwamnan ya kaddamar da fara ginin wata sabuwar Kwalejin Musulunci (High Islamic College) a Fikiyel, wadda aka tsara domin shigar da yaran da ba sa zuwa makaranta, musamman Almajirai, cikin tsarin ilimi na zamani.Yayin da yake jawabi a wurin bikin, Gwamna Zulum ya bayyana cewa Kwalejin Musulunci za ta yi amfani da tsarin karatu na hadaka (hybrid curriculum) bisa jagorancin Hukumar Shirya Jarabawar Larabci ta Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS), inda za a hada ilimin addini da na zamani kamar kimiyya, fasaha, da sauran darussan rayuwa.

“Babban burinmu shi ne mutanen Fikiyel su amfana da wannan makaranta domin muna son shigar da yaran da ba sa zuwa makaranta cikinta, domin su koyi harshen Larabci. Sannan za mu hada tsarin karatun allo (Tsangaya) da tsarin ilimi na zamani ta hanyar gabatar da darussan karatu da rubutu, lissafi, ilimin na’ura mai kwakwalwa, da kuma mafi mahimmanci, koyon sana’o’in hannu,” in ji Zulum.Yayin da yake yi wa gwamnan bayani, Kwamishinan Ilimi, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, ya bayyana cewa an riga an gina irin wadannan kwalejoji na Musulunci a kananan hukumomi 20 na jihar.A wani labarin kuma, Farfesa Zulum ya umarci Ma’aikatar Ilimi ta Jihar da ta kammala shirin mayar da dukkan makarantun sakandaren gwamnati na jihar zuwa na zamani (digitalization).Wannan umarni ya hada da amfani da na’urorin zamani, tsarin koyon karatu ta yanar gizo (e-learning), da kuma azuzuwan zamani (smart classrooms) domin inganta koyarwa da sakamakon dalibai.

Sabbin makarantun biyu da aka kaddamar a Fikiyel da Balbaya, wadanda ke Karamar Hukumar Bayo, kowannensu yana dauke da azuzuwan zamani 20, da dakunan gwaje-gwaje (laboratories), dakin karatu (library), da wuraren wasanni.

 

You might also like
Leave a comment