Gwamnan Sokoto yayi Kira da jami’an tsaro su kawo ƙarshen ƴanbindiga a jahar a 2026

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya buƙaci mutanen jihar da su dage wajen bai wa jami’an tsaro goyon bayan domin magance matsalar hare-haren ƴanbindiga da jihar ke fuskanta ta hanyar taimaka musu da bayanan sirri da sauransu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙonsa na sabuwar shekarar, wanda mai magana da yawunsa Abubakar Bawa ya fitar, inda gwamnan ya ce za su ƙara ƙaimi domin ganin shekarar ta 2026 ta fi 2025 a kowane ɓangare.

“Za mu ci gaba da ba jami’an tsaronmu goyon bayan da suke buƙata domin samun nasara. Mun riga mun fitar da tsare-tsaren da za mu yi musamman wajen tattara bayanan sirri da ganowa tare da daƙile hanyoyin da maharan ke bi wajen kai hare-hare musamman a ƙananan hukumomi 13 da ke fuskantar matsalar.”

Gwamna Aliyu gwamnatinsa za ta muhimmantar inganta ababen more rayuwa a jihar, “kamar yadda suke a ƙunshe a cikin muradunmu guda 9. Sannan za mu inganta sauran ɓangarorin lafiya da jin ƙai da sauransu.”

Ya Kuma   ƙara da cewa za su gina sabbin makarantun Islamiyya, sannan su sabunta tsofaffi, “sannan duk gyare-gyaren da ake yi a makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu duk za mu ba su muhimmanci,” in ji shi, sannan ya ce za su kammala ayyukan wasu manyan titunan jihar kafin ƙarshen rubu’i na farko na sabuwar shekara.

You might also like
Leave a comment