Gwamnatin jahar kano zatafara shirin yaki da cutar zanzabin. tsintsaye (Avian Influenza)

Ma’aikatar Raya Kiwo ta Jihar Kano, karkashin jagorancin    Kwamishina, Dr. Aliyu Isah Aliyu, na shirin fara aiwatar da Kashi na Farko na Shirin Yaki da Cutar Zazzabin Tsuntsaye (Avian Influenza – AI), bayan amincewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

 

 

 

 

Cutar Zazzabin Tsuntsaye, wacce aka fi sani da Bird Flu, cuta ce mai saurin yaduwa tsakanin kaji da sauran tsuntsaye, wacce kan haddasa mace-mace cikin gaggawa tare da jawo asarar   mai yawa ga manoman kiwon kaji.

 

 

 

Domin dakile wannan barazana, Ma’aikatar ta tsara cikakken shiri wanda ya hada da matakan kariya, gano cutar da wuri, karfafa tsauraran ka’idojin tsafta (biosecurity), da kuma samar da hanyoyin daukar matakin gaggawa idan an samu bullar cutar.

 

 

 

 

Shirin na da burin hana bullar cutar, kare manoman kiwon kaji, kiyaye lafiyar al’umma, da kuma karfafa wadatar abinci a Jihar Kano, Najeriya da ma kasashe makwabta.

 

 

 

Dr. Aliyu Isah Aliyu, ya jaddada kudurin Ma’aikatar na daukar matakan rigakafi da kuma aiwatar da ingantattun dabarun shawo kan cututtuka domin kare masana’antar kiwon kaji da bunkasa ci gaban kiwo mai dorewa a Jihar.

 

 

 

 

Kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta Jihar Kano wata alama ce ta hangen nesa da jajircewar Mai Girma Gwamna, Abba Kabir Yusuf, wajen bunkasa harkar kiwo da dakile cututtuka, wanda hakan ne ya haifar da samar da wannan Ma’aikata.

 

 

 

 

A jawabinsa Kwamishina ya mika godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamna bisa cikakken goyon baya da jagoranci da yake bayarwa wajen bunkasa harkar kiwo da kare rayuwa da dukiyar manoma a fadin Jihar Kano.

 

 

 

Sanarwar tafito daga babbar. darantar wayar dakai ta ma,aikatar raya kiwon lafiya ta jahar kano  halima sani gadanya

 

 

← Back

Thank you for your response. ✨

ta Jihar Kano

You might also like
Leave a comment