Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fayyace Gaskiya Kan Shari’ar Victor Solomon, Ta Karyata Jita-jitar Kafafen Sadarwa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada cewa an bi dukkan ka’idojin shari’a yadda ya dace, bisa hujjoji da shaidu na gaskiya inda ta karyata rahotonin kafafen sada zamunta dangane yanke hukuncin.

Da yake jawabi kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke a ranar 6 ga Janairu, 2026, Kwamishinan Shari’a, James A. Kanyip, ya bayyana cewa Victor Solomon ya fuskanci shari’u guda biyu daban-daban a gaban kotuna biyu mabambanta, kan laifuffuka daban-daban da suka shafi mutane daban-daban.
A wata sanarwa da rabawa manema labarai Kwamishinan yace “Babu wani sabani a hukuncin da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta.

“ Victor Solomon an gurfanar da shi ne a shari’u biyu daban. An wanke shi daga zargi a shari’a guda a shekarar 2024, amma kuma an same shi da laifi a wata shari’ar daban a 2026 bisa ga shaidu da aka gabatar a kotu,” in ji Kanyip.

Ya bayyana cewa shari’a ta farko mai Lamba KDH/KAD/73C/2020 wadda ta shafi haɗa baki wajen aikata laifi da yunƙurin aikata kisan kai, ta ƙare da sallamar sa tare da wanke shi daga zargi a ranar 21 ga Mayu, 2024”

“Shari’a ta biyu mai Lamba KDH/KAD/78C/202 ta shafi manyan laifuffuka da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, jikkata mutum ba tare da dalili ba, da kuma kisan kai da ke da hukuncin kisa. An kammala sauraron wannan shari’a a watan Oktoba, 2025, inda daga bisani aka same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 6 ga Janairu, 2026.

“Kotun ba ta yanke hukunci bisa son rai ko dalilan siyasa ba. An bi doka da oda, an gudanar da cikakkiyar shari’a, kuma alkalin kotu ya tantance hujjoji da shaidu yadda ya dace,” in ji Kanyip

Ya ƙara da cewa wanda aka yanke wa hukunci yana da ‘yancin daukaka ƙara har zuwa Kotun Koli kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Da Yane Karin haske kan hukumcin kotun , Kwamishinan Yada Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya gargaɗi jama’a kan yaɗa labaran ƙarya musamman a kan muhimman batutuwan shari’a.

“Yaɗa labaran ƙarya game da hukuncin kotu abu ne mai hatsari. Yana iya tayar da hankalin jama’a da haddasa rikici ba tare da dalili ba. Muna kira ga al’ummar Kaduna da su rika tantance sahihancin labari kafin yadawa,” in ji Maiyaki.

You might also like
Leave a comment