GWAMNATIN JIHAR KANO NA ALHININ RASHIN BARR. MARYAM ABUBAKAR

Gwamnatin Jihar Kano ta sami  labarin rasuwar Barrister Maryam Abubakar, Daraktar Shirye-shirye ta Cibiyar Wayar da Kai kan Shari’a da Accountability (CAJA), tay I matukkar  girgiza. Rasuwarta Barr maryam babban rashi ne ba ga iyalanta kaɗai ba, har ma da ɓangaren shari’a da daukacin al’ummar ƙungiyoyin farar hula.Marigayiya Barrister Maryam kwararriyar lauya ce mai kishin aiki, kuma mai fafutukar tabbatar da adalci, gaskiya, da haƙƙoƙin mata. Sadaukarwar da ta yi wajen haɓaka bin doka da oda, adalci a cikin al’umma, da kyakkyawan shugabanci ya sanya ta zama mace mai hidima, wacce za a yi kewar gudunmawar da ta bayar ƙwarai da gaske.A madadin Gwamnatin Jiha, ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Alh. Abba Kabir Yusuf, na miƙa saƙon ta’aziyya ga shugabanni da ma’aikatan Cibiyar Wayar da Kai kan Shari’a da Accountability (CAJA), Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya (FIDA), Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) rashen jahar Kano da karamar Hukumar Ungogo, da daukacin iyalan ƙungiyoyin farar hula a Kano, da kuma iyalan mamaciyar. Lallai wannan rashi ne mai raɗaɗi wanda ya haifar da gibi mai wuyar cikewa.Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya jikanta yasa ta hutu na har abada a Jannatul Firdaus, sannan ya ba iyalanta, abokan aikinta, da sauran abokan arziki haƙurin jure wannan rashi da ba shi da madadin.Sa hannu:

Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya

Mai Girma Kwamishina,

Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida

29 ga Disamba, 2025

You might also like
Leave a comment