Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Kariya Ga Cibiyoyin Lafiya A Faɗin Ƙananan Hukumomi 44
Gwamnatin Jihar Kano, ta hanyar Cibiyar Dakile Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), ta raba kayan kariya na musamman (PPE) ga dukkan cibiyoyin lafiya da asibitoci da ke faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar, bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Cibiyar Dakile Cututtuka ta Kano, Muhammad Dayyabu, ya fitar tare da raba wa manema labarai a yay Alhamis.“A matsayin nuna jajircewa ga bangaren lafiyar al’umma da kuma shirin tunkarar gaggawa, gwamnatin Najar kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta hanyar KNCDC ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar, Farfesa Muhammad Abbas, ta raba kayan kariya ga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar ta hanyar jami’an sa ido da bayar da rahoton cututtuka (DSNOs),” yace kayayyakin da aka raba muhimman kayan aiki ne ga ma’aikatan lafiya na sahun gaba wajen rigakafi da tunkarar cututtuka. Kayayyakin sun haɗa da rigunan kariya (aprons), takunkumin fuska (face masks), tabarau na kariya (goggles), safar hannu (hand gloves), da maganin kashe ƙwayoyin cuta (sanitizers), da sauran su
Darakta-Janar na KNCDC, Farfesa Muhammad Abbas, wanda ya yi magana a madadin Gwamna Yusuf, ya jaddada cewa samar da kayan kariya yana da matuƙar muhimmanci wajen kare ma’aikatan lafiya da kuma tabbatar da martani cikin gaggawa da inganci yayin bukatar hakan.Ya ƙara da cewa, maimakon tara kayayyakin a babban birnin jiha, Gwamna Yusuf ya tsara raba su zuwa asibitoci da cibiyoyin lafiya a faɗin ƙananan hukumomi 44 don ba da damar tunkarar ɓullar cututtuka cikin sauri,
.Darakta-Janar ɗin ya yaba wa shugabannin ƙananan hukumomi kan haɗin kan da suka bayar, sannan ya nanata kiran da gwamnan ga kafafen yaɗa labarai, sarakunan gargajiya, malaman addini, da shugabannin al’umma da su ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin Jiha da Cibiyar Dakile Cututtuka ta Kano wajen ƙarfafa rigakafin cututtuka da wayar da kan jama’a akan lafiya.