Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da sake gina babbar kasuwar jihar

 

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da sake gina kasuwar jihar da ta yi gobara shekaru biyar da suka gabata.

Yayin ƙaddamar da sake gina kasuwar, Gwamna Ahmad Aliyu ya bayana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin jihar da ta gabata ta kasa sake gina kasuwar, maimakon hakan ma ta bayar da wani ɓangare na filin kasuwar jingina ga wani banki.

Gwamnan ya ce yadda kasuwar ke bayar da gagarumar gudunmowa a fagen tattalin arzikin jihar bai kamata a wofantar da ita ba.

A watan Janairun 2021 ne dai babbar kasuwar ta Sokoto ta gamu da iftila’in mummunar gobara, lamarin da ya jefa ƴan kasuwa da dama cikin mawuyacin hali, yayin da wasu suka koma wasu kasuwannin.

”Bayan da gwamnatinmu ta zo ta kafa kwamitin bincike, inda bayan dogon nazari gwamnati ta ƙudiri aniyar biyan kuɗin jinginar, inda kawo yanzu muka kammala biya, kasuwar ta kuma dawo hannunmu”, in ji shi.

You might also like
Leave a comment