Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabbin hanyoyin magance Satar jarabawar WAEC Da NECO

 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da wasu sabbin dabaru masu tsauri da nufin dakile satar amsa da sauran maguɗan jarabawa a WAEC da NECO, matakan da za su fara aiki daga shekarar 2026.

‎Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, inda suka ce an ɗauki matakan ne domin maido da sahihanci, gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin ilimi a Najeriya.

‎A cewar wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar, gyare-gyaren sun shafi dukkan matakan gudanar da jarabawar ƙasa, daga shirya tambayoyi zuwa tantance sakamako.

Sanarwar ta ce gwamnati za ta ƙarfafa amfani da fasahohin zamani, tare da tsaurara matakan kulawa, domin rage satar amsa da sauran laifukan da ke lalata martabar jarabawa.

‎Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka sanar akwai sabon tsarin tsara tambayoyi, inda za a rika jujjuya jerin tambayoyi daga ɗalibi zuwa ɗalibi, duk da cewa tambayoyin iri ɗaya ne.

‎Ma’aikatar ta ce wannan dabara za ta rage damar haɗa baki a ɗakunan jarabawa, tare da tabbatar da cewa kowane ɗalibi na rubuta jarabawa ta musamman.

‎Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada haramcin sauya makaranta a matakin SS3, tana mai cewa za a fara aiwatar da dokar cikin kwanaki masu zuwa, domin dakile sauye-sauyen makaranta na ƙarshe da ake zargin suna da alaƙa da satar jarabawa.

‎Sanarwar ta jaddada cewa dukkan hukumomin jarabawa — ciki har da WAEC, NECO, NBAIS da sauran su — wajibi ne su bi waɗannan ƙa’idoji, domin tabbatar da daidaito da ingancin bayanai a faɗin ƙasar.

‎Bugu da ƙari, ma’aikatar ta ce za a fara amfani da lambar shaidar ɗalibi ta musamman (Examination Learners’ Identity Number), wadda za ta bai wa gwamnati damar bibiyar ɗalibi a duk tsawon tsarin jarabawa.

You might also like
Leave a comment