Gwamnatin Tarayya ta takaita bikin kamalla karatu a marantunta
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da takaita bikin kammala karatu a dukkan makarantun ƙasar, inda ta ce ɗalibai ’yan aji shida na firamare, JSS 3 da SSS 3 kaɗai ne za su rika yin bikin kammala karatu. Gwamnatin ta ce matakin na da nufin rage shagulgula da kuma sauƙaƙa wa iyaye nauyin kuɗi.
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, tare da Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaba Sa’idu, ne suka bayyana matakin. A wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar, an ce wannan na daga cikin gyare-gyaren da ake yi domin inganta harkar ilimi da rage wa iyalai wahala.
Sanarwar ta kuma ce gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon tsari na amfani da littattafan karatu masu inganci da daidaito, waɗanda za su iya ɗaukar shekaru huɗu zuwa shida ana amfani da su. An bayyana cewa matakin zai rage yawan kuɗin da iyaye ke kashewa, ya bai wa ’yan uwa damar raba littattafai, tare da inganta koyarwa da koyo a makarantun faɗin ƙasar.