Gwamnatin Venezuela tana kama masu adawa da Gwamnati
Gwamnatin Venezuela ta zafafa kamen da take yi wa ƴan’adawar siyasa bayan hamɓarar da shugaban ƙasar, Nicolas Maduro tare da kama shi.
Jami’an ƴansandan riƙe da makamai sun zafafa sintiri a kan titunan Caracas, babban birnin ƙasar.
Ministan Shari’ar ƙasar, Diosdado Cabello, ya wallafa wani hoto da ya ɗauka da jami’an tsaron a shafinsa ranar Litinin da daddare.
A ɗaya daga cikin bidiyoyin da ya wallafa an jiyo jami’an tsaron na cewa ”biyayya koyaushe, bijirewa babu”.
Rahotonni na cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya – bisa umarnin gwamnati – na cusguna wa mutane da ke murnar hamɓarar da Maduro a wani harin Amurka.