Hari Bam ɗin Zamfara : ‘Ramuwar-gayya ce ɓarayi ke son yi kan kashe ‘yan uwansu
A zamfara, ana can ana kokarin tantance irin ta’adin da fashewar wasu bamabamai biyu da aka dasa a kan hanyar Dansadau zuwa Gusau a jihar Zamfara, suka yi.
Bayanan da aka fara samu sun nuna cewa mutum goma sha daya suka rasu a fashewar, amma hukumomi sun ce yawan bai wuce mutum bakwai ba.
Ana dai zargin wannan wani salon harin ramuwar gayya ne ‘da ‘yan bindiga suka kaddamar, game da kisan da ‘yan sa-kai suka yi wa wasu ‘yan bindiga da mukarrabansa a makon jiya a yankin.
Yanzu haka dai ana can cikin jimami da zaman jugum, da kuma dakon tantance matafiyan da ko dai suka jikkata ko ma suka rasu sakamakon fashewar