Harin ƙunar baki-wake a masallaci a Syria ya kashe mutum 5
Akalla mutum biyar sun mutu wasu sama da 20 sun jikkata a harin bam din da aka kai wani wani masallaci lokacin da ake sallar Juma’a a birnin Homs da ke kusa da Wadi al-Dhahab na kasar Syria.
BBC ta rawaito cewa harin ya faru ne ana tsaka da sallar juma’a lokacin da masallacin ya cika makil, kuma bam din ya fashe ne daga wani lungun masallacin.
Hotunan da aka yada a intanet sun nuna yadda masallacin ya yi kaca-kaca bangon shi ya lalace. Jami’ai a yankin sun ce suna zargin dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din.
A ‘baya bayanan ana samun karuwar tashin hankali da kashe mutane a hare-haren da ake kai wa birnin Homs, inda mazauna ke kiran a tsaurara matakan tsaro