Harin ƴan tawayen M23 ya kashe fararen hula 1,500 a DR Congo

A jamhuriyar Dimukradiyyar Congo an kashe fararen hula 1500 a Wani sabbin hare-hare da ‘yan tawayen M23 da Rwanda ke marawa baya a kudancin yankin Kivu.

Wata sanarwa da gwamnatin Congo ta fitar, ta ce sojoji da jami’an tsaro ne suka fitar da adadin, duk da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Disamba da ya wuce a Amurka.

Kinshasa ta ce sama da farar hula dubu 500 sun rasa muhallansu, sakamakon kazamin fadan da ya rincabe tsakanin sohin gwamnati da na ‘yan tawaye a yankuna daban-daban na ƙasar.

Tun da fari ‘yantawayen M23 sun janye daga gabashin yankin Uvira, inda suka ce matakin na cikin yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranta, to amma da alama fada ya sake dawowa.

You might also like
Leave a comment