Hukumar Kula da asibitoci ta Jahar kano ta dakatar da likitocin da suka manta almakashi a cikin mara lafiya

Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta ce ta tabbatar da zargin da aka yi na cewa ma’aikatan lafiya sun bar almakashi a cikin wata mata mai suna Aishatu Umar a lokacin tiyata, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta daga bisani.

Wata sanarwa da aka fitar na cewa Babban Sakataren Hukumar Dr. Mansur Mudi Nagoda ya dakatar da ma’aikatan da lamarin ya faru a lokacin aikinsu tare da gabatar da batun a gaban kwamitin ladabtarwa.

Sannan Kuma Hukumar ta ce ta dakatar da ma’aikata uku waɗanda suke da hannu a cikin lamarin nan take.

Haka kuma, sanarwar ta ce an miƙa batun ga kwamitin ladabtarwa ga ma’aikatan lafiya a jihar domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace waɗanda dokoki suka tanada.

Hukumar ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar kan abin bakin ciki da ya faru.

Ta tabbatar da cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba kuma za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare rayuka da kuma samun amincewar marasa lafiya a faɗin cibiyoyin lafiya na jihar.

You might also like
Leave a comment