Hukumar Yan sanda tace Ba za ta fitar da bayanai kan hare-haren Amurka a Sokoto ba

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa tana da bayanai kan hare-haren da Amurka ta kai kan ’yanbindiga a arewa maso yammacin jihar Sokoto, amma ba za ta fitar da su ga jama’a ba.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels.

Hundeyin ya ce: “A matsayinmu na rundunar ’yan sanda, mun san wasu abubuwa game da hare-haren, amma ba za mu yi magana a kai ba.”

Ya kuma kara da cewa an tura jami’an ’yan sanda domin tabbatar da tsaro a yankunan da hare-haren suka shafa, musamman bayan samun rahotannin cewa wasu fararen hula na iya samun rauni ko rasa rayukansu.

A ranar 25 ga Disamba, 2025 ne Amurka ta kai hare-hare kan ’yanbindiga a Sokoto, inda Ma’aikatar Tsaron Amurka ta bayyana cewa “yanbindiga masu alaƙa da ISIS da dama” sun rasa rayukansu a hare-haren da aka gudanar bisa umarnin gwamnatin Najeriya.

A jiya Talata ne rundunar sojin Amurka a nahiyar Afirka (Africom) ta sanar cewa ta miƙa wa Najeriya kayan aikin soja domin tallafawa yaki da matsalar tsaro.

 

Ba za mu fitar da bayanai kan hare-haren Amurka a Sokoto ba – Ƴansanda

You might also like
Leave a comment