Hukumar zabe mai zaman kanta ta inec ta sauya ranar zaɓen shugaban kasa dan na yan majalinsa shekarar 2027

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC)  ta sanya sabbin ranakun gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma na ’yan majalisun tarayya da na jihohi na kasar na 2027.

 

 

 

Hakan na zuwa ne mako biyu bayan hukumar ta fitar da jadawalin zaben na farko, wanda ya sha suka daga bangarori da dama kasancewar ranakun da hukumar ta sanar za su iya fadawa cikin watan azumin Ramadana na shekarar 2027.

 

 

 

 

Lamarin ya kai ga cewa majalisar dokokin kasar ta yi gyara ga dokar zaben kasar game da lokaci mafi kankanta na sanar da ranar gudanar da zabe.

 

 

 

 

 

A jadawalin farko da hukumar ta fitar, ta sanya ranar 20 ga watan Fabarairun 2027 a matsayin ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, sai kuma 6 ga watan Maris 2027 a matsayin ranar zaben gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.

 

 

 

 

 

 

Sa dai a cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Fabarairun 2025, wadda ta samu sa hannun shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a Mohammed Kudu Haruna, ta ce: “bayan yin gyara ga dokar zabe ta 2022, da kuma amincewa da dokar zabe ta 2026, hukumar ta yi gyara tare da sauye-sauye ga lokutan shirye-shiryen zabe da kuma na zabukan domin ya yi daidai da tsarin sabuwar doka”.

 

 

 

 

You might also like
Leave a comment