INEC ta Fara Rijistar masu zabe karo na biyu
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta fara mataki na biyu na aikin rijistar masu zaɓe a fadin Najeriya bayan kammala mataki na farko a hukumance ranar 10 ga Disamba, 2025.
Aikin ya fara ne daga jiya, Litinin, inda hukumar ke bai wa ‘yan Najeriya damar yin rajista ta intanet ko ta hanyar gaba da gaba a cibiyoyin rijistar zaɓe da aka keɓe
INEC dai ta fara rajistar zaɓe ta intanet ne a ranar 18 ga Agusta, 2025, sannan ta fara rajistar gaba da gaba daga 25 ga Agusta, 2025.
A mataki na farko, mutum miliyan 9,891,801 ne suka fara rajista ta intanet daga ciki mutum miliyan 2,572,054 ne suka kammala rajistarsu gaba ɗaya, inda mutum miliyan 1,503,832 suka kammala ta intanet yayin da kuma mutum 1,068,222 ta gaba da gaba.
Sai dai hukumar ta jaddada za a ci gaba da dakatar da aikin rijistar zaɓen a jihar Anambra da Babban Birnin Tarayya, Abuja saboda wasu muhimman ayyukan zaɓe da ke gudana.