Jam iyyar adawa ta PDP za ta kai APC kotu kan zaɓen Abuja
Jam’iyyar PDP ta sanar da kafa wata ƙungiyar lauyoyi ta musamman domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a yankunan babban birnin tarayya, Abuja.
Matakin na zuwa ne bayan sakamakon da INEC ta bayyana ya nuna cewa ‘yan takarar APC sun lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi biyar cikin shida.
APC ta yi nasara a ƙananan hukumomin Abaji da ƙaramar hukumar birni wato AMAC da Bwari Kwali da Kuje, yayin da PDP ta samu nasara a Gwagwalada kaɗai. An gudanar da zaɓen ne domin cike kujerun shugabanni shida da na kansiloli 62.
Jam’iyyar ta ce zaɓen ya gudana cikin yanayi na rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a da kuma rahotannin sayen ƙuri’u.
A sanarwar da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Ini Ememobong, ya fitar, jam’iyyar ta taya waɗanda suka yi nasara murna amma ta jaddada cewa akwai kura-kurai a sakamakon.
Ta bayyana cewa ƙungiyar lauyoyinta za ta kasance ƙarƙashin jagorancin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na ƙasa, Shafi Bara’u, tare da kira ga duk ‘yan takarar da ke da ƙorafi su gaggauta gabatar da su domin ɗaukar mataki.